Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, shafin yanar gizo na Annaba na kungiyar Daesh ya sanar da cewa, kungiyar ta Daesh ce ke da alhakin kaddamar da farmaki kan jami'an tsaron kasar Saudiyya a ranar Lahadin da ta gabata a wani wurin tsari a yankiin Buraidah, da ke arewacin birnin Riyad fadar mulkin masarautar Al Saud.
Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar saudiyya ta sanar a ranar Lahadin cewa, wasu 'yan bindiga uku ne suka kai harin, inda suka halaka daya daga cikin jami'an tsaro, yayin su ma jami'an tsaron sun halaka biyu daga cikin maharan.
Kungiyar Daesh dai kungiya ce da ke dauke da akidar wahabiyanci, kuma tana kafirta duk wani musulmi da bai shiga cikin kungiyar ba tare da halasta jininsa.